James 4

Miƙa Kanku ga Allah

1Me yake jawo faɗace-faɗace da gardandami a tsakaninku? Ashe, ba shaʼawace-shaʼawacenku da suke yaƙi a zukatanku ba ne? 2Kukan nemi abu ku rasa, sai ku yi kisa da ƙyashi. In kuka rasa abin da kuke nema sai ku shiga yin gardama da faɗa. Kukan rasa ne, domin ba ku roƙi Allah ba. 3Saʼad da kuka roƙa, ba kwa samu, don kun roƙa da mugun nufi, don ku kashe abin da kuka samu a kan shaʼawace-shaʼawacenku.

4Ku mazinata, ba ku san cewa abokantaka da duniya gāba ce da Allah ba? Duk wanda ya zaɓa yǎ zama abokin duniya ya zama abokin gāban Allah ke nan. 5Ko kuna tsammani a banza ne Nassi ya ce ruhun da ya sa yǎ zauna a cikinmu yana kishi sosai? 6Amma yakan ba mu alheri a yalwace. Shi ya sa Nassi ya ce,

“Allah yana gāba da masu girmankai
amma yakan ba da alheri ga masu tawaliʼu.”
K Mag 3.34

7Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah. Ku yi tsayayya da Iblis, zai kuwa guje ku. 8Ku matso kusa da Allah shi kuwa zai matso kusa da ku. Ku wanke hannuwanku, ku masu zunubi, ku kuma tsarkake zukatanku, ku masu zuciya biyu. 9Ku yi baƙin ciki, ku yi makoki ku kuma yi kuka. Ku mai da dariyarku ta zama makoki, farin cikinku kuma yǎ zama ɓacin zuciya. 10Ku ƙasƙantar da kanku a gaban Ubangiji, zai kuwa ɗaukaka ku.

11ʼYanʼuwa, kada ku ɓata wa juna suna. Duk wanda ya zargi ɗanʼuwansa ko ya ɗora masa laifi, yana gāba da doka ne yana kuma yin mata shariʼa ke nan. In kuwa ka ɗora wa shariʼa laifi, kai ba mai binta ba ne, mai ɗora mata laifi ne. 12Akwai Mai ba da doka da kuma Alƙali guda ɗaya tak, shi ne yake da ikon ceto da kuma hallakarwa. Amma kai-wane ne da za ka hukunta maƙwabcinka?

Yin Fahariya game da Gobe

13Yanzu fa sai ku saurara, ku da kuke cewa, “Yau ko gobe za mu je wannan ko wancan birni, mu yi shekara a can, mu yi kasuwanci, mu ci riba.” 14Alhali kuwa ba ku ma san abin da zai faru gobe ba. Wane iri ne ranku? Ku kamar hazo ne da yake bayyana na ɗan lokaci saʼan nan yǎ ɓace. 15A maimakon haka, ya kamata ku ce, “In Ubangiji ya yarda, muna kuma a raye, za mu yi wannan ko wancan.” 16Ga shi, kuna fariya da taƙama. Duk irin wannan taƙama mugun abu ne. 17Saboda haka, duk wanda ya san abu mai kyan da ya kamata yǎ yi, bai kuwa yi ba, ya yi zunubi ke nan.

Copyright information for HauSRK